Luke 18

Misali na Gwauruwa Mai Naciya

1Yesu ya faɗa wa almajiransa wani misali, don ya koya musu yadda ya kamata su dinga yin adduʼa kullum, ban da fasawa. 2Ya ce, “A wani gari, an yi wani alƙali wanda ba ya tsoron Allah, bai kuma kula da mutane ba. 3A garin nan kuma, akwai wata gwauruwa, wadda ta dinga zuwa wurin alƙalin nan, da roƙo cewa, ‘Ka ba ni adalci tsakanina da maƙiyina.’

4“An daɗe yana ƙi, amma a ƙarshe ya ce cikin tunaninsa, ‘Ko da yake ba na tsoron Allah, ba na kuma kula da mutane ba, 5amma don gwauruwan nan ta dame ni, zan tabbatar cewa ta sami adalci, domin kada ta gajiyar da ni, da yawan zuwanta.’ ”

6Sai Ubangiji ya ce, “Ku ji fa abin da alƙalin nan, marar gaskiya, ya ce. 7Ashe, Allah ba zai biya wa zaɓaɓɓunsa da suke masa kuka, dare da rana adalci ba? Zai ci gaba da ƙin sauraronsu ne? 8Ina gaya muku, zai tabbatar sun sami adalci, ban da ɓatan lokaci. Amma saʼad da Ɗan Mutum ya dawo, zai sami bangaskiya a duniya ke nan?”

Misali na Bafarisiye da Mai Karɓar Haraji

9Yesu ya kuma faɗi wannan misali ga waɗansu masu taƙama da adalcinsu, kuma suna rena sauran mutane, ya ce, 10“Waɗansu mutane biyu sun tafi haikali don yin adduʼa. Ɗaya Bafarisiye ne, ɗayan kuma mai karɓar haraji. 11Sai Bafarisiyen ya tashi tsaye, ya yi adduʼa game da kansa yana cewa, ‘Allah, na gode maka, saboda ni ba kamar sauran mutane ba ne, wato, mafasa, masu aikata mugunta, masu zina, ko kuma kamar mai karɓar harajin nan. 12Ina azumi sau biyu a mako, ina ba da zakka daga kowane abin da na samu.’

13“Amma mai karɓar harajin ya tsaya daga nesa. Bai ma iya ɗaga kansa sama ba, sai ya buga ƙirjinsa, yana cewa, ‘Allah, ka yi mini jinƙai, ni mai zunubi ne.’

14“Ina gaya muku, wannan mutum ne, ba ɗayan ba, ya koma gida baratacce, babu laifi a gaban Allah. Gama duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi. Wanda kuma ya ƙasƙantar da kansa, za a ɗaukaka shi.”

Yesu da Ƙananan Yara

15Mutane suna kawo jarirai wurin Yesu don ya taɓa su. Da almajiransa suka ga haka, sai suka kwaɓe su. 16Amma Yesu ya kira yaran a wurinsa, ya ce, “Ku bar yara ƙanana su zo wurina. Kada ku hana su, gama mulkin Allah na irin waɗannan ne. 17Gaskiya nake gaya muku, duk wanda ba zai karɓi mulkin Allah kamar ƙaramin yaro ba, ba zai taɓa shiga mulkin ba.”

Mai Mulki Mai Arziki

18Wani mai mulki ya tambayi Yesu, ya ce, “Malam managarci, me zan yi don in gāji rai madawwami?”

19Yesu ya amsa, ya ce, “Don me kake kira na managarci? Ai, babu wani managarci, sai Allah kaɗai. 20Ka san dokoki da suka ce, ‘Kada ka yi zina, kada ka yi kisankai, kada ka yi sata, kada ka ba da shaida ta karya, ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka.’ ”

21Mutumin ya ce, “Ai, tun ina ƙarami, na kiyaye duka waɗannan.”

22Da Yesu ya ji haka, sai ya ce masa, “Akwai abu ɗaya har yanzu da ya rage maka. Ka sayar da duk abin da kake da shi, ka ba wa matalauta, saʼan nan za ka sami dukiya a sama. Bayan haka, ka zo ka bi ni.”

23Da jin haka, sai ya ɓata rai, domin shi mai arziki ne sosai. 24Yesu ya kalle shi, ya ce, “Yana da wuya fa, masu arziki su shiga mulkin Allah! 25Hakika, zai fi sauƙi raƙumi ya shiga ta ƙofar idon allura, da mai arziki ya shiga mulkin Allah.”

26Mutanen da suka ji wannan magana suka tambaya suka ce, “To, in haka ne, wa zai iya samun ceto?” 27Yesu ya amsa, ya ce, “Abin da ba ya yiwuwa ga mutane, mai yiwuwa ne ga Allah.”

28Sai Bitrus ya ce, masa, “To, ga shi mun bar kome da muke da shi, don mu bi ka!”

29Yesu ya ce musu, “Gaskiya nake gaya muku, ba wanda ya bar gida, ko mata, ko ʼyanʼuwa maza, ko iyaye, ko yara, saboda mulkin Allah, 30da zai kāsa samun riɓi mai yawa, a wannan zamani, ya kuma sami rai madawwami a zamani mai zuwa.”

Yesu Ya Sāke Magana a kan Mutuwarsa

31Sai ya kai Sha Biyun gefe ɗaya, ya ce musu, “Za mu Urushalima, kuma dukan abin da annabawa suka rubuta a kan Ɗan Mutum zai cika. 32Za a ba da shi ga Alʼummai, za su yi masa baʼa, su zage shi, su tofa masa miyau, su yi masa bulala, su kuma kashe shi, 33a rana ta uku kuma zai tashi.” 34Almajiran ba su gane da ko ɗaya daga cikin wannan ba. An ɓoye musu maʼanarsa, kuma ba su gane da abin da yake magana a kai ba.

Makaho Mai Bara Ya Sami Ganin Gari

35Da Yesu ya yi kusa da Yeriko, akwai wani makaho da yake zaune a gefen hanya, yana bara. 36Da ya ji taron suna wucewa, sai ya yi tambaya ko mene ne ke faruwa. 37Suka ce masa, “Ai, Yesu Banazare ne ke wucewa.”

38Sai ya yi kira, ya ce, “Yesu, Ɗan Dawuda, ka yi mini jinƙai!”

39Mutane da suke gaba suka kwaɓe shi, suka ce masa ya yi shiru. Amma sai ya ƙara ɗaga murya, yana cewa, “Ɗan Dawuda, ka yi mini jinƙai!”

40Sai Yesu ya tsaya, ya ba da umarni a kawo mutumin wurinsa. Da ya zo kusa, Yesu ya tambaye shi, ya ce, 41“Me kake so in yi maka?” Sai ya amsa, ya ce, “Ubangiji, ina so in sami ganin gari.”

42Yesu ya ce masa, “Ka sami ganin garinka. Bangaskiyarka ta warkar da kai.” 43Nan da nan, ya sami ganin garinsa, kuma ya bi Yesu, yana yabon Allah. Da dukan mutane suka ga wannan, sai su ma suka yabi Allah.

Copyright information for HauSRK